27 Yuli 2014 - 07:39
Boko Haram sun kashe sojojin Kasar Kamaru 4 a jiya asabar

A kalla sojojin kasar Kamaru 4 ne su ka rasa rayukansu a wani hari da ‘yan kungiyar Boko Haram su ka kai musu

 Kamfanin Dillancin Labarun Reuters ya ambato   wata sanarwa da  Sojan  kasar ta Kamaru su ka fitar a jiya asabar da a cikin su ka bayyana cewa: Kungiyar ta Boko Haram ta kai wasu hare-hare har sau biyu a cikin kasar a bayan nan. Wani jami’in sojan kasar ta Kamaru mai suna Flix Naji Fozomkong ya ce: A wani harin da ‘yan Boko Haram din su ka kai a garin Bargaram sun kashe sojojin kasar 4. Kawo ya zuwa yanzu dai kasar Kamarun ta kara girke sojojinta da su ka kai 1000 a kusa da iyaka da Najeriya. ABNA